A Armeniya 'yan jam'iyyar adawa sun yi yunkurin yi wa magajiyar gari wanka da kashi

A Armeniya, 'yan jam'iyyar adawa sun far wa magajiyar garin Erivan da kwalabe cike makil da kashi,da nufin watsa mata a fuska, saboda ta ki tsaftace magudanan ruwan kwalbati,wadanda suka cika makil,wanda hakan yasa doyi ke ci gaba da addabar su.

Kwalaben sun kubuce daga hannu, a daidai lokacin da 'yan siyasar ke gaf da kai wa babbar magajiyar ,Taron Markaryan hari, inda nan take zauren majalisar dokokin kasar wanda aka kebe da zummar gudanar da taro, ya turnike da wari.

Wannan doyin ya haifar da somewar shugaban jam'iyyar Republicain, Mariya Baragamyan wanda aka garzaya da shi asibiti

'Yan sanda da likitocin halayyar bil adama sun yi kadaran-kadahan don kawo wa Misiz Taron dauki tare da katse hanzarin maharan.

'Yan adawar sun bayyana cewa, manufarsu ita ce koya wa magajiya Taron hankali, saboda da halin ko-in-kula da nuna game doyin da ke ci gaba da illata lafiyarsu da ta 'ya 'yansu.

Tag: Duniya

Labarai masu alaka