Amurka ta ware dala miliyan 500 a kasafin kudin bana don taimaka wa 'yan ta'adda

Ma'aikatar Tsaro ta Amurka Pentagon ta bayyana ware dalar Amurka miliyan 500 a kasafin kudin bana don taimakawa 'yan ta'addar PKK/YPG/PYD da ke Siriya.

Rahoton da Pentagon ta fitar game da Siriya ta bayyana cewa, a kasafin kudin bana an samu karin dala miliyan 70 sama da na shekarar da gabata.

Pentagon ta ware dala miliyan 433 domin samar da bama-bamai, bindigu, motocin yaki, tankoki da makaman kariya daga makamai masu linzami ga 'yan ta'addar da ke Siriya.

Sauran dala miliyan 67 kuma za a yi amfani da shi wajen samar da magunguna ga 'yan ta'addar. 

Amurka ba tana bayar da taimakon makamai da kayan yaki ga 'yan ta'addar ba ne kawai, tana kuma kara yawan su. 

Rahoton ya ce, nan da ƙarshen shekara za a kara yawan 'yan ta'addar zuwa dubu 30 daga dubu 25 da suke a yanzu.

A shekarar 2019 kuma Amurka za ta ware dala miliyan 550 domin yaki da 'yan ta'addar Daesh inda za a ba wa PKK/PYD/YPG horo. 

Tag: PYD , PKK , Dala , Amurka

Labarai masu alaka