Amurka da Rasha na gaf da fara gwabza yaki

Dakarun kawancen kasashen duniya da Amurka ke wa jagoranci da suke kai wa 'yan ta'addar Daesh hare-hare a Siriya sun kai wani kan motar yaki mallakar Rasha.

Amurka da Rasha na gaf da fara gwabza yaki

Dakarun kawancen kasashen duniya da Amurka ke wa jagoranci da suke kai wa 'yan ta'addar Daesh hare-hare a Siriya sun kai wani kan motar yaki mallakar Rasha.

Kakakin kawancen kasashen Kanal Ryan Dillon ya bayyana cewa, a ranar 10 ga watan Fabrairu wata tankar yaki ta Rasha ta kai wa kawancen kasashen hari a kauyen Tebiye da ke lardin Dauruzzor na kudancin Siriya.

Dillon ya ce, Amurka ta kai wa tankar ta Rasha samfurin T-72 hari ne don kare kanta.

Dillon ya kara da cewa, domin kauce wa bacin rana suna tattauna wa da bangaren Rasha amma bai bayyana ko motar ta waye ba.

Tag: Rasha , Siriya , Hari , Amurka

Labarai masu alaka