Halin da Al'umar Yammacin Thrace suke ciki a Girka

Turkawan Yammacin Thrace: Tir da tilasta wa mutane bin sabbin al’adu da akidoji.

Halin da Al'umar Yammacin Thrace suke ciki a Girka

Matsalolin Kasashen Duniya: 07

Zamu yi nazari kan sharhin Farfesa Kudret Bülbül,Shugaban Tsangayar Nazarin kimiyyar siyasa Ta Jami’ar Yildirim Beyazıt da ke Ankara.

Turkawan Yammacin Thrace: Tir da tilasta wa mutane bin sabbin al’adu da akidoji.

Ku yi tunani na dan wani lokaci. Duk yadda kuka gabatar da kanku ta kowace tsiga, (Bajamushe,Balarabe,Baturke,Musulmi,Kirista,Zindiki da dai sauran su),a kasar da kuka rayu sama da shekaru dubu, gwamnati ta ce muku " Ku ba haka kuke ba",kazalika "Babu wata al'uma da ke wannan kasar duba da yadda kuka gabatar da kanku.Mece ce alakar gwamnati da yadda mutane suka gabatar da kansu ? Kamata yayi kasashe su amince,kana su karrama yadda al'umomi suka gabatar da kansu.Kamar zaku ce : "A wannan karnin babu wani abu mai kama da hakan".Ina matukar bukatar in ce muku "Gaskiyarku, wannan karkatacciya fahimta mai nasaba da akidar Farkisanci ba za ta taba kasancewa a wannan karnin ba.Watakil,ragowan misali ne na tarihi".Amma kash ba hakan abun yake ba.Saboda wannan lamarin, na ci gaba da wanzuwa a daya daga cikin kasashen Tarayyar Turai, wato Girka.Sama da shekaru dubu,mutane na ci gaba da gwagwarmayar ganar da gwamnatin Girka cewar,a kasar akwai mutane da ke gabatar da kansu a matsayin Musulman Turkawa.Ina magana ne game da matsalar Turkawan Thrace, wadanda ke rayuwa a Girka tun gabanin kafuwar daular Musulunci ta Usmaniyya.Bayan gushewar wannan daular,Turkawan Thrace sun kasance a karkashin kariyar dokokin kasa da kasa na kare hakkokin kabilumarasa rinjaye,bayan wasu yarjejeniyoyi da aka yi.Amma abin bakin ciki, yawancin wadannan hakkokin sun kasance kan takarda ne kawai.A yau,zan tabo daya daga cikin wadannan hakkokin da aka yi wancakali da su.

Gurbataccen Lamiri

Babu makawa, dukannin hakkokin da suka jibanci siyasa,tattalin arziki, al'ada da dai sauransu na da muhimmanci sosai. Amma 'yancin mutum na bayyana kansa kamar yadda yake bukata, yana daya daga cikin hakkokin farko.Saboda yana da alaka da kasancewarsa bil adama.Duba da ayar doka ta 6 ta yarjejeniyar kare hakokkin bil'adama ta kasa da kasa, "Duk inda mutum zai kasance,kamata yi shari'a ta yi na'am da yadda ya bayyana kansa".Yadda mutun zai gabatar da kansa, abu ne na tsakanin mutum da karan kansa,babu ruwan gwamnati da wannan.Domin wani bangare da ke manne da mutuncinsa, kana ba za a iya sadaukarwa ko yin watsi da shi ba.Yin wancakali da al'ada da kuna akidojinsa,yin inkari ne da kuma salwantar da mutuncinsa.Watakil shi yasa marubuci Emil Maaluf a cikin littafinsa na " Miyagun Al'adu" ya ja hankalinmu,inda ya ce al 'adar mutum, na da nasaba ne da wurin da aka fi raunana shi.Domin duk mutumin da aka yi watsi da al'adarsa, zai zage damtse a wajen kalubalantar duk wata barazana, don ganin ya gabatar da kansa.Namijin kokarin da Musulmai da Kiristan farko suka yi, a wajen gwagwarmaya da zaluncin da suke fuskanta da nufin bayyana kansu, wani babban misali ne.

Kin amince da kasancewar Turkawa

Matsalolin da ke wakana game da kasancewar Turkawa a yammancin Thrace bai sha bamban da wannan ba.Daga shekarar 1927, a lokacin da aka kafa kungiyar "Hadakan Turkawan Xanthi" har ya zuwa wajejen shekarar 1980, komai ya ci gaba tafiya salim-alim.A shekarar 1983, jami'an tsaro sun saudakar da allon da ke makale a kofar kungiyar, saboda akwai kalmar "Turk" a rubutun da ya kunsa.Daga bisani aka hana kungiyar gudanar da aiyukanta.Kananan kotuna da babban kotun Girka sun rufe ta hanyar cewa "Babu Turkuwa a Thrace".Abinda yasa aka garzaya da matsalar Musulman yammacin Thrace a gaban kotun kare hakkin bil Adama na Turai.A shekarar 2008, kotun ta bai wa kungiyar "Hadakan Turkawan Xanthi" gaskiya.Amma a cewar dokokin girka wannan matakin na kotun kare hakokkin bil adama ba za ta haifar da da mai ido ba kai tsaye, kamata yayi a dukufa zuwa dokokin cikin gida.Shekaru 10 kenan da Turkawan Thrace ke ci gaba da gwagwarmaya don ganin Girka ta tabbatar da matakin da kotu kare hakkoki bil adama ta Turai a aikace.Zaman kotu na karshe an yi shi ne a a ranar 9 ga watan Fabrairun shekarar bana a Gümülcine na yankin Thrace,amma kawo yanzu babu wani sakamako.Shekaru 35 kenan da ake ci ga da gudanar yakin tabbatar da daya daga cikin muhimman hakkokin bil adama,wanda aka fara a shekarar 1983.Turkawan yammancin Thrace na ci gaba da gwagwarmaya ba tare sun tsalake iyakokin da dokoki suka shimfida ba.Shekaru 35 kenan da suke jiran adalci daga Girka da kuma kotun kare hakokkin bil adama ta Turai wacce kawo yanzu bata taba yi wa gwamnatin wannan kasar matsin lambar da ta kamata ba.Akasin haka,shari'ar Girka na ci gaba da samar da hanyoyin toshe baki, mamaikon tabbatar da gaskiya.

Ranar tsayayya ta kasa

A ranar 29 ga watan Janairun shekarar 1998,Turkawan Thrace sun gudanar da wani gaggarumin taro don yin Allah wadai da matakin kotunan Girka na yin nuni da halin ko-in-kula da lamarinsu.An ayyana wannan ranar a matsayin "Ranar Tsayayya ta Kasa".Amma Girka ta zabi tarwatsa wannan taro da kuma hana shirya dukannin wasu shagulgulan da suka gangance ta.A ranar tsayayya ta shekarar 1990, duk da yunkurin hana Turkawa taruwa, dubban mutane sun yi fito dafifi don bayyana wa duniya kawunansu da kuma al'adunsu.A yayin shagulgulan wannan taron mai hallaci ta fuskar demokradiyya da kuma shari'a,Girkawa masu tsatsaurin ra'ayi sun kai wa Tukawan Thrace farmakai.Tsawon kwanaki 2,an farfasa shaguna tare da wawushe dukiyoyinsu.Haka zalika,an jikkata Turkawa da dama,wadanda a ciki har da Muftin yankin Xhanti, Mehmet Emin Ağa da dan majalisar yankin,Ahmet Faikoğlu.A wannan zamanin, 'yan sandan kasar Girka zuba ido kawai suka yi suna kallo.

Ga inkarin kasancewar Turkawa kawai, lamarin ya tsaya ?

Abin bakin ciki ne,amma matsaloli a Girka ba su tsaya kan kin amincewa da kasancewar Turkawa kawai ba.Duk da an shimfida yarjejeniyoyi duba da amincewar juna,daruruwan dubban Turakawan Thrace na fama da rashin samun 'yancin zaben mufti,kuntatawa a ibada,tsangwama wajen mallakar dukiya da hajoji,yin watsi da mutuncinsu,kin mayar musu da arzikin da aka wawushe a hannunsu, takukunmi a fannin ilimi,da dai sauran su.Masu kwankwanto game da matsalolin da Turkawan yammancin Thrace ke fuskanta, za su iya leka rahotannin da Hukumar kare hakkokin bil adama da Jam'iyyar Katip Çelebi ta wallafa a harsunan Turkanci,Girkanci da Ingilishi.Dukannin wadannan take hakkoki, suna wakana ne a daidai lokacin da Turkiyya ta yi manya-manyan ababen alheri kamar su,yi wa cocin Akdamar kwaskwarima tare da bude shi ga masu ibada,sake dawo da yankin haykalin Mor Gabriel,fara karantarwa a makarantar Romawa ta Gökçeada da kuma daukar nauyin sake gina cocin Bulgeriyawa na birnin Santambul.Wani sashe na wannan matsalar,shi ne,kama daga cibiyoyin Tarayyar Turai ya zuwa kungiyoyin kasa da kasa, babu wanda ya taba yin wani abin a zo a gani, a wajen hana afkuwar wannan zaluncin.A daya gefe kuma, duniyar Islama ta jahilci wannan batun.

Abun da ya fi kuna zuciya kuma, shi ne duk da kwakwaru da kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama na Turkiyya,sun tanadi sani marar misaltuwa game da matsalolin kare hakkin bil hakkin da suka jibanci fararen hular kasarsu,amma kusan za'a iya cewa ba su san komai ba game da zaluncin da ke afkuwa a Girkwa, wacce ke gaf da Turkiyya.Muna fatan,aiyuka kamar rahotanni game da take hakkin bil adama a Girka su yawaita sosai.Haka zalika al'umarmu ta tanadi cikakken sani game kan wannan batun tare ganin zalunci ya argu a doron duniya.

Mun gabatar muku da sharhin Farfesa Kudret Bülbül, shugaban tsangayar kimiyyar siyasa ta jami’ar Yıldrım Beyazıt da ke birnin Ankaran kasar Turkiyya.Labarai masu alaka