"Mun nunawa duniya Qudus nada maga isa"

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan a jawabinsa na taron ƙolin ƙasashen Musulmi akan Qudus ya bayyana cewar birnin Qudus nada maga isa wadanda zasu kareta kuma matakin Trump ya saɓa wa doka kuma gurguwar dabara ce.

Erdoğan ya bayyana cewar a wannan taron namu mu nunawa duniya da cewar Qudus nada maga isa.

Taron da aka gudanar a birnin Istanbul ya samu halartar shugaban ƙasar Falasɗinu Mahmud Abbas, Sakataren Tarayyar Ƙasashen Musulmi Yusuf Bin Ahmed Al Useymin inda suka gudanar da taron manema labarai.

Erdoğan ya bayyana cewar wannan matakin da Trump ya ɗauka na nuni da cewa Amurkan bazata iya sulhunta rikicin Falasɗinu da lsra'ila ba. Yayinda ya ƙara da cewa wannan gurguwar mataki ce kuma babu nazari ko kima acikita.

Daga ƙarshe Erdoğan ya jinjina wa matasa, mata da yaran da suka fito don ƙalubantar wannan zalunci lsra'ila. An kuma bayyana gabashin Kudus a matsayar babban birnin Falasdinu a taron.Labarai masu alaka