Tambaya Da Amsa

Tambayarmu a wannan watan ita ce kamar haka:

A ranar 18 ga watan Nuwamban 2017 zakaran wansan daga abubuwa masu nauyi dan kasar Turkiyya wanda ya yi fice a duniya da nahiyar Turai Naim Sulaymanoğlu ya rasu, shin sau nawa yana karya bajinta a duniya?

  1.  Sau 36
  2.  Sau 46
  3.  Sau 56

Za a bada kyaututtuka ga mutane 3 da suka sami nasarar amsa wannan tambaya dai-dai. Za kuma a zabe su ne ta hanyar yin canke bayan sun aiko da amsar tasu.

Za ku iya turo da amsoshinku har nan da karshen watan Disamba. Sai ku ziyarci shafinmu na yanar gizo na trt.net.tr/hausa don cike gurbin amsar tambayar tare da aiko wa.

Sai mun ji daga gare ku. Daga nan TRT Hausa Muryar Turkiyya.


Amsa Tambayawar Wannan Watan