Comey: Trump makaryaci ne, ga yaudara kuma ba shi da cikakken hankali

Tsohon Shugaban Hukumar Bincike ta Amurka FBI James Comey ya bayyana cewa, Shugaban Amurka Donald Trump ba shi da dabi’u masu kyau a saboda haka bai cancanci zama shugaban Kasarsu ba.

Tun bayan da Trump ya kori Comey wannan ne karo na farko ya yi hira da kafar talabijin ta ABC inda kan littafin da ya rubuta wanda ya soki Truöp a cikinsa.

Comey ya yi tallan littafin nasa mai suna “Biyayya mai Tsanani” wanda ya rubuta shi game da Trump din.

Ya ce, ya kamata shugaba ya zama mai gaskiya, amma wannan shugaban na Amurka ba sh, da gaskiya. Duba da hankalinsa bai cancanci zama Shugaban Amurka ba.

Ya kara da cewa, Trump ne mutum mai daukar mata a matsayin wani bangare na nama, mai fadar karya a koyaushe kan kanana da manyan batutuwa inda ya ke tunanin Amurkawa na aminta da abin da ya ke fada.

Comey ya kuma ce, Trump zai ci amanar duk wani da ya ke tare da shi.

Tsohon shugaban na FBI ya kuma tabo batun tsohon mai ba wa Trump shawara kan sha’anin tsaro Michael Flynn da aka kora inda ya ce, Trump ya nemi da ya dakatar da bincikar Flynn wanda hakan ke nuni kara zuwa ga kokarin hana tabbatar da adalci.Labarai masu alaka