'Yan ta'addar Houthi na Yaman da Iran ke taimakawa sun kai wa Saudiyya hari da makami mai linzami

Yan ta’addar Houthi ‘Yan Shi’a na Kasar Yaman da Iran ke mara wa baya sun sake kai hari da makami mai linzamia garin Jazan na na Saudiyya.

Kakakin kawance Kasashen Larabawa da ke kai wa ‘yan ta’addar hare-hare a Saudiyya Kanal Turki Al-Maliki ya bayyana cewa, an yi amfani da garkuwar makamai masu linzami wajen lalata makamin tun kafin ya fado kasa.

Ya ce, an hari unguwar fararen hula da makamin kuma babu wanda ya mutu ko jikkata daga buraguzansa bayan an lalata shi.

A ranar Alhamis din nan ma ‘yan ta’addar na Houthi sun kai wa Saudiyya hare-hare da makamai masu linzami 3.

Tun shekarar 2014 ne mayakan Houthi suka kwace wasu biranen Yaman da suka hada da San'a Babban Birnin Kasar inda suka yi kokarin kifar da gwamnati.

A watan Maris din shekarar 2015 kuma Saudiyya ta jagoranci Ƙasashen Larabawa wajen kai wa Houthi hare-hare ta sama a Yaman.Labarai masu alaka