An gano kashin dan yatsan dan adam mai shekaru dubu 85 a Saudiyya

A wani rahoto da aka buga a mujallar "Ecology and Evolution" mai buga bincike kan halittu an bayyana cewa, a yankin Al-Wusta na Saudiyya an samu kashin dan yatsan dan adam mai shekaru dubu 85.

An gano adadin shekarun dan yatsan bayan binciken da masana suka gudanar.

An bayyana cewa, idan har aka kammala bincike kuma aka tabbatar da shekrun kashin haka suke, to zai zama na mutum na farko da ya fara rayuwa a tsibirin Larabawa.

Masaniya kan rayuwar dan adam ta jami’ar Griffith Julien Louys ta bayyana cewa, wannan na nuna cewa, shekaru dubu 85 zuwa dubu 90 da suka gabata mutane sun rayu baya ga a nahiyar Afirka da gabashin tekun Mediterrenean.Labarai masu alaka