Amurka na ci gaba da girbar abin da ta shuka

Mutane 17 ne suka mutu sakamakon bude wuta a wata makarantar Sakandire da ke jihar Florida ta Amurka.

Amurka na ci gaba da girbar abin da ta shuka

Mutane 17 ne suka mutu sakamakon bude wuta a wata makarantar Sakandire da ke jihar Florida ta Amurka.

An kama maharin mai suna Nikolas Cruz wanda tsohon dalibin makarantar ne wadda ke garin Broward na jihar ta Florida. An kori dalibin a shekarar da ta gabata bayan ya yi laifi.

Sanarwar da 'yan sanda suka fitar ta bayyana cewa, Nikolas ya fara kashe mutane 12 a cikin makarantar, sannan bayan ya fita ya sake harbe mutane 2 da ke waje, a hanyarsa ta gudu wa ya harbe mutum 1 sai wasu 2 da suka mutu bayan kai su asibiti.

An bayyana cewa, maharin ya yi amfani da bindiga samfurin AR-15 wajen kai harin.

Hukumar FBI ta Amurka ta fara gudanar da bincike kan lamarin.

Bayan afkuwar lamarin Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka mutu.


Tag: Ajali , Cruz , Hari , Amurka

Labarai masu alaka