Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi ta bayyana Kudus a matsayin Helkwatar Falasdin

Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi OIC ta bayyana jawabin bayan taron gaggawa da ta y a birnin Istanbul na Turkiyya inda ta ce, Kudus Babban Birnin Kasar Falasdin ne.

Kiran da Shugaban Kasar Turkiyya ya yi a jawabinsa na neman Kasashen Duniya su ayyana Kudus a Matsayin Helkwatar Falasdina ya fito a sanarwar bayan taron.

Kasashen na Musulmi sun yi kira ga sauran Kasashen Duniay da su mayar da martani kan wanna batu da Amurka ta yi.

Sanarwar ta yi suka da Allah Wadai game da ayyana Kudus a matsayin Helkwatar Isra'ila da Amurka ta yi. 

An fada wa Amurka cewa, lallai ta janye wannan mataki ko kuma duk abin da ya faru to ita ce da alhaki.Labarai masu alaka