"In da hannun saudiyya a batan Kashoggi,to ta gama yawo"

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi wa kasar Saudiyya Barazana,inda ya ce,idan har gwamnatin Riyadh na da hannu dumu-dumu a batn dan jarida Jamal Khashogi,to ta gama yawo.

Shugaban na Amurka ya furta wannan kalamin a tashar talabijin CBS News,a ranar Asabar din nan da ta gabata.

Trump ya ce, " Akwai yiwuwar Sa'udiyyawa na da hannu a batan Kahshoggi.Idan har Amurka ta gano hakan, to babu kamawa sai sun dandana kudarsu.Wannan lamari ya matukar muni,saboda wanda ya bace dan jarida ne".

CBS ta dau alkwarin wallafa cikakken bayanin na Trump kan batun Khashoggi a gobe,Lahadi.

Jamal Khashoggi ya yi layar zana a ranar 2 ga watan Oktoba, bayan ya shiga ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Istanbul na Turkiyya.

Budurwar Khashoggi,Hatice Cengiz ta ce ta rake shi ofishin jakadanci,kuma ta tatabatar da cewa ya shiga amma bai fito ba.

Amma shugabannin Saudiyya sun watsi da wannan maganar,inda suka dan jaridar ya shigo,inda ya fita kai-tsaye.Labarai masu alaka