"Don Allah Boko Haram ki sakar mana Leah"

A ranar Jumma'ar nan da ta gabata manyan malaman kasar Najeriya sun roki Boko Haram da ta sako wata matashiya Kirista mai suna Leah Sharibu,wacce take ci gaba da kasancewa a hannun kungiyar ta'addar,sabili da ta ki musulunta.

"Don Allah Boko Haram ki sakar mana Leah"

A ranar Jumma'ar nan da ta gabata manyan malaman kasar Najeriya sun roki Boko Haram da ta sako wata matashiya Kirista mai suna Leah Sharibu,wacce take ci gaba da kasancewa a hannun kungiyar ta'addar,sabili da ta ki musulunta.

Leah dai ta kasance daga cikin 'yan mata 112,wadanda Boko Haram ta yi garkuwa da su a watan Fabrairun da ya gabata.

Kafafan yada labaran Tarayyar Najeriya sun sanar da cewa,'yan kungiyar Boko Haram sun saki kawayen Leah,amma sun ki su sako ta,saboda ta ki rungumar addinin Musulunci.

A 'yan kwanakin nan Boko Haram ta sanar wa duniya cewa,za ta yanke wa matashiyar hukunci kisa a tsakiyar watan Oktoban bana,inda har gwamantin Najeriya ba ta cika wasu sharuda da ta gindaya ma ta ba.

Yayin wani taron manema labarai, fasto Yukubu Pam ya ce:

"Dan Allah Boko Haram ki sakar mana da 'yan matan kika yi garkuwa da su.Saboda basu da wani laifi.Kuma ina ganin idan kika yi haka,Najeriya ga baki daya za ta yi fara'a sosai".

Sheikh Muhammad Khalid kuma cewa ya yi:

"Mun samu labarin cewa mako mai zuwa, shi ne wa'adi na karshi kafin suka kashe ta.Shi yasa muke tattauna batun zaman lafiyar Najeriya.Saboda akwai matukar muhimmanci mu tattauna wannan batun.Mahaifiya da kuma 'yan uwan Leah na cikin halin ukuba.Muna gama su da Allah.Da fatan zai Allah zai tausasa zukatansu don su watsi da aniyarsu".

Khalid ya sanar da cewa dukannin ababen da 'yan Boko Haram suka yi sun yi hannun riga da karantarwar addinin Musulunci,inda ya kira shugabannin Najeriya da su dauki matakan kwato Leah daga hannun 'yan ta'adda,inda ya ce:

"Muna son mu fahimtar kowa cewa, wadannan 'yan ta'addar da ke sace 'ya 'yanmu da kuma wasu mutane na daban ba Musulmai ba ne.Isalam ba ta umarni da a yi garkuwa da bayin Allah.Zamu hade kai don ganin mu hana 'yan Najeriya fadawa tashin hankali.Muna rokon su da syi karatun ta-natsu don sako mana wadanda suka sace,musamman Leah Sharibu".Labarai masu alaka