Jami’an tsaron Najeriya sun kasha ‘yan bindiga 35 a jihohin Kasar 4

‘Yan bindiga 35 ne suka mutu sakamakon farmakan da jami’an tsaron Najeriya suka kai musu a jihohin Kasar 4 daban-daban.

Jami’an tsaron Najeriya sun kasha ‘yan bindiga 35 a jihohin Kasar 4

‘Yan bindiga 35 ne suka mutu sakamakon farmakan da jami’an tsaron Najeriya suka kai musu a jihohin Kasar 4 daban-daban.

An bayyana cewa, an kama wasu mutanen da dama a farmakan da sojojin Najeriya suka kai a yankunan da ake samun rikici tsakanin manoma da makiyaya.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya rawaito mukadddashin darakatan yada labaran ma’aikatar tsaron kasar John Agim na cewa, a jihohin Benue, Taraba, Zamfara da Nassarawa sojoji sun kai wa ‘yan bindiga farmakai.

Agim ya kara da cewa, an kashe ‘yan bindinga 35 a farmakan tare da kama wasu da dama inda aka kuma kwace makamai daga hannunsu.

Agim ya kuma ce, an yi garkuwa da soja 1 inda aka kuma jikata wasu 2.

 Labarai masu alaka