UNICEF: Za a saki yara kanana 200 da aka tirsasa yaki a Sudan ta Kudu

Asusun Tallafawa Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana cewa, kungiyoyin da ke rikici da juna a Sudan ta Kudu za su saki yara kanana sama da 200 da suka saka a yaki.

Sanarwar da ofishin UNICEF ya fitar ta bayyana cewa, a ranar Talatar nan za a saki akalla yara kanana 207 ‘yan kasar Sudan ta Kudu inda za amika wa iyayensu su.

Sanarwar ta ce, za a taimaka wa yaran da za a saki da abinci da kuma gyara kwakwalensu.

A watan Fabrairu ne a karkashin jagorancin UNICEF aka saki yara 311 a Sudan ta Kudus.

A rahoton da helkwatar UNICEF ta fitar a shekarar da ta gabata an bayyana cewa,  akwai yara kimanin dubu 19 da aka saka a harkokin yaki a Sudan ta Kudu.

A shekarar 2011 Sudan ta Kudu ta balle daga Sudan inda bayan shekaru kasar ta fada yakin basasa bayan shugaban Kasar Salva Kiir ya kori mataimakinsa Riek Machar bayan zargar sa da yunkurin shirya masa juyin mulki.Labarai masu alaka