Masu neman fansa sun yi garkuwa da Bajamushe a Kano

An yi garkuwa da wani Injiniya Bajamushe a jihar Kano da ke arewa maso-gabashin Najeriya.

Masu neman fansa sun yi garkuwa da Bajamushe a Kano

An yi garkuwa da wani Injiniya Bajamushe a jihar Kano da ke arewa maso-gabashin Najeriya.

Kakakin 'yan sandan jihar Kano Magaji Musa Majiya ya ce, an yi garkuwa da Michael Cremza wanda Injiniyan aikin hanyoyi ne a Kano.

Majia ya kara da cewa, masu garkuwar sun kashe dan sanda 1 da ke tsaron lafiyar Bajamushen a lokacin da ya yi kokarin tsare shi.

A jihohin Najeriya da yawa ana garkuwa da mutane domin neman fansa.

Duk da cewa, akwai dokar yanke hukuncn kisa ga masu garkuwa da mutane amma duk dahaka lamarin bai sauya ba.Labarai masu alaka