Masar ta cire sunayen mutane 299 daga jerin sunayen 'yan ta'adda

Kotun Kolin Masar ta dauki matakin cire sunayen mutane 299 daga jeriin sunayen 'yan ta'adda.

Masar ta cire sunayen mutane 299 daga jerin sunayen 'yan ta'adda

Kotun Kolin Masar ta dauki matakin cire sunayen mutane 299 daga jeriin sunayen 'yan ta'adda.

Kamfanin dillancin labarai na Masar ya bayyana cewa, a shari'ar "'Yan ta'addar Daesh" da ake yi ne kotu ta saka sunayen wasu 'yan kasar ta Masar 299 a jerin sunayen 'yan ta'adda amma bayan lauyoyinsu sun daukaka kara sai kotun koli ta ta cire sunayen.

Kotun kolin ta yanke hukuncin a sake kai mutanen wata kotun ta daban don sake duba Shariar tasu tun daga farko.

A ranar 1 ga watan Yunin 2017 ne kotun hukunta manyan laifuka ta Alkahira  ta sanya sunayen mutane 299 a jerin sunayen wadanda ake zargi da zama mambobin kungiyar ta'adda ta Daesh.

A ranar 15 ga watan Agustan shekarar lauyoyinsu suka daukaka kara.

An zarge su da zama mambonin daesh, kashe 'yan sanda a tsibirin Sİnai da kuma mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.


Tag: Hukunci , Daesh , Masar , Kotu

Labarai masu alaka