Cutar Ebola ta fara addabar rogo

Manyan masu bincike kan sha'anin noma na kasashen duniya 12 sun gano cewa, nahiyar Afirka na gaf da fama da barazanar yunwa,sabili da cutar Ebola da ta fara addabar rogo.

africa.jpg
Ebola.jpg

Manyan masu bincike kan sha'anin noma na kasashen duniya 12 sun gano cewa, nahiyar Afirka na gaf da fama da barazanar yunwa,sabili da cutar Ebola da ta fara addabar rogo.

Afirka dai ita ce ta farko wajen shuka rogo,inda kusan kashi 57 na al'umarta,wato mutum milyan 80 ke amfani da shi a matsayin abincin yau da kullum.

Amma a 'yan shekarun nan, wata kwayar cutar wacce masana suka kira da "Ebolar rogo" ta dinka yaduwa a ,inda ta lalata kusan kashi 90 zuwa 100 na gonakin rogo.

Abinda yasa masu bincike na kasashe 12 suka kira da a dauki matakan gaggauwa kafin wannan annobar ta jefa Afirka cikin matsanancin yunwa.

"Muna kiran shubaganni da su gaggauata daukar kwararan matakan kauda wannan annobar tun kafin wankin hula ya kai mu dare" inji Justin Pita shugaban cibiyar bincike kan yaduwar kwayoyin cututtuka a nahiyar Afirka ta Yamma, (WAVE).

Corneille Ahanhanzo, mai bincike a kasar Jamhuriyyar Benin kuma cewa ya yi,

"A gaskiya, ba a ware isasshen lokaci da kuma kudi ba wajen gudunar da bincike mai zurfi don kauda wannan annobar ba.Shi yasa kamata ya yi,tun yanzu masanan Afirka su daura damarar yakar wannan cutar,ko kuma mu ciza yatsa nan da wani matsakaicin zamani".

A Gabashin Afirka ma, tuni masana suka gano wannan cutar wacce a yanzu haka take ci gaba da yaduwa ba tare an samu maganinta ba.

A Najeriya, kasar da ta fi kowace yawan mutane a Afirka, kusan kashi 80 cikin dari na al'umarta ne ke amfani da rogo a matsayin cimakar yau da kullum.

AFP

 Labarai masu alaka