Ambaliyar ruwa ta kashe mutane da dama a Tanzaniya

Mutane 15 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a Darussalam Babban Birnin Kasar Tanzaniya.

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane da dama a Tanzaniya

Mutane 15 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a Darussalam Babban Birnin Kasar Tanzaniya.

Kwamishinan yanki Paul makonda ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce, an rufe makarantu don kauce wa sake samun mutuwar was mutanen.

A arewacin garin Mwanza mutane 2 sun mutu.

Hukumar Kula da Yanayi ta Tanzaniya ta yi gargadin cewa, za a samu mamakon ruwan sama a yankuna da dama da suke kusa da tekun Indiya wadanda suka hada da tsibiran Zanzibar, Darussalam, Tanga, Lindi da Mtwara.

Mutanen da suke zaune a unguwannin da ke gangare ne ambaliyar ruwan ta fi shafa.

Makonde ya bukaci al’umar da su koma yankuna masu tudu don zama.

 Labarai masu alaka