Wani kasurgumin maciji ya sake hadiye Naira miliyan 23 a ofishin JAMB a Najeriya

Kwanaki kadan da aka fitar da rahoto mai ban mamaki na cewa, maciji ya hadiye Naira miliyan 36 a ofishin Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami'o'i ta Najeriya a jihar Benue, a yanzu ma wani jami'in hukumar ya ce, katin Naira miliyan 23 ya kone a motarsa.

A wannan karon jami'in Hukumar JAMB a jihar Nassarawa Labaran Tanko ya ce, motarsa ta kone a lokacin da ya ke dauke da katin zana jarrabawar na Naira miliyan 23.

Amma Hukumar ta ce, ba za ta amince da ikiririn Mista Tanko ba kamar yadda ta yi watsi da batun jihar Benue.

Hukumar ta ce, bayan gudanar da bincike ta gano an yi amfani da katinan da Tanko ya yi ikirarin sun kone a motarsa duk da cewa, ya mika musu rahoton da ya karba daga wajen 'yan sanda.

Kwanakin da suka wuce ne akawun ofishin sayar da katin rubuta jarabbawar ta JAMB da ke jihar Benue Philomina Chieshe ta bayyana cewa, maciji ya hadiye Naira miliyan 36 na kudaden da aka sayar da katin.

Najeriya dai kasa ce da ta dade tana fama da matsalar cin hanci da Rashawa.Labarai masu alaka