Mummunan hatsarin mota ya yi ajalin dalibai 22 a jihar Kano da ke arewacin Najeriya

Akalla dalibai 22 ne suka mutu sakamakon wani mummunan hatsarin mota daya afku a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

Mummunan hatsarin mota ya yi ajalin dalibai 22 a jihar Kano da ke arewacin Najeriya

Akalla dalibai 22 ne suka mutu sakamakon wani mummunan hatsarin mota daya afku a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

Lamarin ya afku a ranar Talatar da ta gabata a lokacin da motar bas din da ke dauke da daliban ta yi taho mu gama da wata babbar mota a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa yawon bude ido don karo ilimi.

Kakakin 'yan sandan jihar Kano Magaji Musa Majiya ya shaida cewa, baya da wadanda suka mutu, wasu daliban sun jikkata.

Majiya ya rawaito wani da ya shaida lamarin na cewa, dukkan motocin na kokarim kauce wa ramukan kan hanyar a lokacin da suka yi karo da juna.

Lamarin ya so ya janyo hayaniya a yankin amma kuma jami'an tsaro sun kwantar da hankulan mutane.

Rashin kyawun hanyoyi a Najeriya na yawan kashe mutane da ke cikin ababan hawa.Labarai masu alaka