Kotu ta aika da wasu 'yan ta'addar Boko Haram gidan maza bayan yanke musu hukunci

Kotu a yankin arewa maso gabashin Najeriya ta yanke hukuncin daurin shekaru 2 zuwa 15 ga wasu mambobin kungiyar ta'adda ta Boko Haram su 20.

A wata sanarwa da kakakin ma'aikatar shari'a ta kasar Salihu Musa ya fitar an bayyana cewa, rukunin alkalai 4 daban-daban ne suka yanke hukuncin a kotun gwamnatin Tarayya inda aka kuma aika da 'yan ta'addar zuwa gidan yarin garin Kainji.

Jami'an Najeriya sun ce, a ranar Litinin din nan ne aka dawo da shari'ar sama da 'yan ta'addar dubu 1,000 wanda ake sa ran kammalawa nan da wasu 'yan kwanaki. A watan Oktoban bara ne aka yi shari'ar wasu mambobin kungiyar su 45.

Kotun ta Tarayya ta kuma yanke hukuncin daurin shekaru 15 ga wani Haruna Yahaya mai shekaru 35 saboda rawar da ya taka wajen sace 'yan matan Chibok a shekarar 2014. 

Isa ya kuma ce, za a saki akalla mutane 468 da ake tsare da su saboda ba a samu wata hujjar cewa, suna da alaka da kungiyar ba wadanda za kuma a ba suy horo ta yadda za su dawo cikin al'umunsu lafiya.Labarai masu alaka