• Bidiyo

'Yan kunar bakin wake sun kashe mutane 14 a Najeriya

Akalla mutane 14 ne suka mutu yayinda wasu 29 suka samu raunuka sakamakon harin kunar bakin wake a birnin Maiduguri da ke arewa maso-gabashin Najeriya

Maharan su 4 sun nufi taron jama'a da ke yankin Muna Gari a birninna Maiduguri.

Kakakin 'yan sandan jihar Borno Victor Isuku ya ce, 'yan kunar bakin da suka hada da mata 2 da maza kuma ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe kawunansu tare da mutane 14. 

Jimillar mutane mutane 18 da suka hada da 'yan ta'addar ne suka mutu, a cewar Isuku.

Ya kara da cewa, dan ta'adda na farko ya tayar da bam din a wajen da ake Sallah inda sauran kuma suka tayar da nasu a wurare daban-daban a yankin.

Ya kuma ce, an jikkata wasukarin mutane 29 a harin wadanda ake ci gaba da kula da lafiyarsu a asibiti.Labarai masu alaka