Sojin Zimbabwe na ci gaba da tattaunawar ganin Mugabe ya sauka daga mulki

Rundunar Sojin Zimbabwe ta bayyana cewa, tana ci gaba da tattauna wa tare da tuntubar masu ruwa da tsaki don ganin shugaban kasar Robert Mugabe ya sauka daga kan mulki.

Rundunar sojin bayan ta gana da Mugabe ta fitar da wata sanarwa a jaridar the herald ta kasar inda suka ce, an samu nasarar kassara mutanen da suka kewaye shugaba Mugabe, kuma suna ci gaba da tattauna wa don ganin ya sauka daga kan mulki.

A ranar Alhamis din nan Mugabe da ke tsare a gida ya gana da shugaban rundunar sojin Zimbabwe Janaral onstantino Chiwenga.

Wakilan Afirka ta Kudu sun halarci ganawar inda bayan haka suka dauki hoto tare da Mugabe.

A ranar Laraba ne sojin Zimbabwe suka yi wa Harere babban birnin kasar kawanya inda suka sanar da cewa, kokarin sauke Mugabe ba wai juyin ulki ba ne.Labarai masu alaka