Sojojin Zimbabwe sun kwace iko da Harare babban birnin kasar, sun musanta yin juyin mulki

Sojojin Zimbabwe sun kwace iko da kafar talabijin ta kasar da ke birnin Harare inda a safiyar Larabar nan suka fitar da sanarwa ta tashar.

Kakakin rundunar sojin Manjo Janar SB Moyo ne ya yi jawabi ta kafar talabijin din ta Zimbabwe inda ya ce, sun soke duk wani hutu da jami'an soja suke yi aciki da wajen kasar, suna kira ga dukkan sojoji da su koma bariki nan take. Shugabanninsu na musu kallon masu tsare kasa, al'adu, da al'uma baki daya.

Sanarwar ta kuma ce, shugaba Robert Mugabe da iyalansa na nan kalau, amma sojojin na farautar muggan mutanen da ke tare da shi.

Wannan lamari ya afku ne bayan ganin tankokin yaki a Zimbabwe na dosar Harare babban birnin kasar inda mutane suka fara fargabar ko juyin mulki za a yi.

Haka zalika sojojin sun yi kira ga shugaba Mugabe da ya dakatar da kora da cusgunawa wasu 'yan jam'iyyarsa da ya ke yi, in kuma ba haka ba to sojojin za su toma hannu a mulkin kasar.Labarai masu alaka