Mutane da dama sun mutu a wani mummunan hatsarin mota a Itopiya

Mutane 21 ne suka mutu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya afku bayan hantsilawar wata motar bas a kasar Itopiya.

Mutane da dama sun mutu a wani mummunan hatsarin mota a Itopiya

Mutane 21 ne suka mutu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya afku bayan hantsilawar wata motar bas a kasar Itopiya.

Kamfanin dillancin labarai na Itopiya ENA ya bayyana cewa, lamarin ya afku a yankin Atsbi Wenberta da ke jihar Tigray ta arewacin Itopiya a lokacin da motar bas dauke da fasinjoji 34 ta hantsila bayan sitiyari ya kwace wa matukinta.

Kwamishin 'yan sanda mai kula da harkokin sufuri na yankin Gebremedhin Nrea yace, mutane 21 sun mutu a motar wadda ta dauki fasinjoji sama da ka'ida.

 Labarai masu alaka