• Bidiyo

Kungiyar Kasashen Kudancin Afirka ta yi taron gaggawa game da Zimbabwe

Kungiyar Cigaban Kasashen Kudancin Afirka (SADC) ta gudanar da taron gaggawa game da yunkurin kifar da gwamnatin kasar Zimbabwe.

Kungiyar Kasashen Kudancin Afirka ta yi taron gaggawa game da Zimbabwe

Kungiyar Cigaban Kasashen Kudancin Afirka (SADC) ta gudanar da taron gaggawa game da yunkurin kifar da gwamnatin kasar Zimbabwe.

Sanarwar da Kungiyar ta fitar ta ce, ministocin harkokin waje na kasashen Angola,Tanzaniya, Zambiya da Afirka ta Kudu ne suka halarci taron wanda aka gudanar a Jamhuriyar Bostvana.

A yayin taron an tattauna batun halin da Zimbabwe ta shiga inda kwanaki 2 da suka gabata sojoji suka sauke shugaba Robert Mugabe tare da tsare shi a gida.

Kungiyar ta Cigaban Kudancin Afirka na da mambobi 15 wanda ta ke aiyukan cigaba da warewa rikicin siyasar yankin.Labarai masu alaka