Gwamantin Sanagal ta mika wa Turkiyya makarantun FETO

Gwamnatin Kasar Sanagal ta mika wa Asusun Ma'arif da gwamnatin Turkiyya ta kafa makarantun 'yan ta'addar Fethullah FETO da ke kasar tare da ba su umarnin gudanar da harkokinsu.

A shekarar da ta gabata ne aka kafa Asusun Ma'arif domin karbe makarantun 'yan ta'addar daga hannun tare da tafiyar da harkokinsu.

Tun bayan yunkurin juyin mulkin 15 ga Yulin 2016 Turkiyya ta yi kira ga gwamnatocin kasashen duniya da su rufe makarantun FETO wadanda suke da hannu a yunkurin, tare da neman a mika mata dukkan makarantunta.

Wani rahoto da Hukumar Leken Asirin Turkiyya ta fitar a watan Mayu ya ce, 'yan ta'addar na FETO na da makarantu, kafafan yada labarai, Asibitoci, Kungiyoyi masu zaman kansu da na 'yan kasuwa 2,800 a kasashe 170 na duniya.

A ranar Talatar da ta gabata ne gwamnatin Sanagal tare da Asusun Ma'arif suka sanya hannu kan yarjejeniyar mika makarantunga Asusun.Labarai masu alaka